Dakile CORONA: Ganduje Ya Tsawaita Hutu Ga Ma’aikata

Gwamnatin jihar Kano ta kara baiwa ma’aikatan ta hutun makonni biyu domin su ci gaba da zama a gida sakamakon dakile yaduwar cutar Coronavirus a fadin jihar.

A jiya ne dai Gwamnatin karkashin jagorancin Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ta sanar da karin hutun.

Sakataren yada labaran gwamnan Kano, Abba Anwar shine ya fitar da sanarwar mai kunshe da sa hannunsa.

An dai kara kwanakin ne bayan cikar wa’adin hutun makwanni biyu wanda gwamnatin ta bayar a baya sakamakon dakile yaduwar cutar ta Coronavirus a Kano.

Related posts