Dakarun Soji Sun Yi Wa ‘Yan Bindiga Kisan Kiyashi A Hanyar Abuja

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar a wani martani na musamman, jami’an tsaro sun aika dandazon yan bindiga lahira, waɗan da suka addabi matafiya a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

An ruwaito cewa jami’an tsaron sun ɗauki wannan matakin ne bayan umarnin da shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ba hafsoshin tsaro na gamawa da ‘yan Bindigan.

A wani bidiyo da muka samu, ya nuna gawarwakin yan bindigan masu tarin yawa da dandazon tarin Babura suna ci da wuta.

Wata majiya daga jami’an tsaro, ta bayyana cewa ana cigaba da jibge jami’ai da suka haɗa da sojoji, yan sanda, da jami’an fasaha a wasu kauyuka dake kan babbar hanyar ta Kaduna zuwa Abuja.

“Tun kafin shugaban ƙasa ya bada umarni aka fara jibge jami’an tsaro amma umarnin yasa aka kara turo jami’ai da dama, da kayan aiki yakar yan bindigan.”

“Zuwa yanzun an kashe sama da yan bindiga 12 waɗan da suka yi kokarin tserewa da suka ga sojoji sun fara shawagi.” “Mafi yawan yan bindigan da aka kashe suna da hannu a sace matafiya na kwanan nan domin mutanen yankin sun gane fuskokin gawarwakin.”

A ranar Alhamis, shugaban kasa Buhari ya umarci hafsoshin tsaro su kawo karshen yan bindiga da yan ta’addan da suka hana zaman lafiya a Najeriya. Shugaban ya ba su wannan umarnin ne a taron majalisar koli kan tsaro, ya kara da cewa kada su rintsa har sai yan Najeriya sun iya bacci cikin kwanciyar hankali.

Labarai Makamanta