Dakarun Soji Sun Yi Wa Boko Haram Kisan Kiyashi

Rundunar sojojin Nijeriya sun bayyana cewa sun yi yi artabu da ‘yan Boko Haram a yankin ƙaramar hukumar Marte dake jihar Borno.

Jaridar PRNigeria ta ce sojojin sun yi musayar wuta da ƴan ta’addan a jiya Talata yayin da suka ƙaddamar da farmaki domin kakkaɓe mayaƙan na Boko Haram a garuruwan Hausari da Missene da Chikungudu da ke cikin ƙaramar hukumar Marte.

Sai dai jaridar ta ruwaito cewa an kashe sojojin Najeriya biyu yayin da bakwai suka samu rauni.

Amma dakarun na Najeriya sun yi nasarar ƙwato bindiga ƙirar AK47 guda 27 da wasu manyan bindigogi masu harbo jirgin sama guda uku da motocin yaƙi biyu daga hannun mayaƙa
Tare da hallaka Mayakan na Boko haram sama da 30.

Allah ya kara baiwa sojojin Kasar mu nasara.

Labarai Makamanta