Dakarun Soji Sun Hallaka ‘Yan Bindiga Da Dama A Dajin Zamfara

Rahotannin dake shigo mana da hukumar tsaro ta ƙasa na bayyana cewar Jami’an tsaron haɗin guiwa sun hallaka yan bindiga aƙalla 32 a dajin Zamfara wanda ya yi iyaka da jihar Neja, inda suka hallaka ‘yan Bindiga da dama waɗanda suka tsero daga Zamfara.

Wannan ya biyo bayan harin da yan bindigan suka kaiwa jami’an tsaro, inda suka harbe yan sanda 5 har Lahira, waɗanda suka yi kokarin maida martani.

Gumurzun ya faru ne a ƙauyen Bangu Gari, dake ƙaramar hukumar Rafi ta jihar Neja ranar Lahadi, kamar rahotanni suka tabbatar.

Wata majiya daga cikin jami’an tsaro ya bayyana cewa wasu yan bindiga da suka fito daga Zamfara saboda ruwan wutan sojoji, sun fara kafa sansani a yankin.

“Adadi mai yawa na yan bindigan ɗauke da muggan makamai, ciki harda roket, sun tattaru a yankin bayan tserowa daga sansaninsu dake Danjibga da Munhaye a ƙaramar hukumar Tsafe, jihar Zamfara.”

Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigan sun farmaki caji ofi ɗin yan sanda dake Bangu Gari, ƙaramar hukumar Rafi, inda suka hallaka jami’ai 5.

“Nan take bayan samun rahoton faruwar haka jami’an tsaron haɗin guiwa suka nufi wurin domin kai ɗauki.” “A ƙarin karfi kuma sojoji sun yi wa yan ta’addan kwantan bauna yayin da suka yi kokarin tserewa ta hanyar garin Tegina.”

“Aƙalla mutum 32 sojojin suka kashe, cikinsu harda shugabanninsu, Karki Buzu da Yalo Nagoshi, yayin da wani babban ƙasurgumin dan ta’addan, Ali Kawaji, ya samu muggan raunuka.”

Labarai Makamanta