Daina Biyan Kudin Fansa Ne Maganin ‘Yan Bindiga – Mustapha Inuwa

Sakataren gwamnatin jihar Katsina Mustapha Inuwa ya bayyana cewar ba abu bane mai yiwuwa ‘yan bindiga su daina ta’addanci muddin jama’a na cigaba da biyan kudin fansa.

Mustapha Inuwa ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da manema labarai da ya yi a fadar gwamnatin Jihar Katsina dangane da ƙaruwar yin garkuwa da mutane a yankin Arewa.

Sakataren gwamnatin yace biyan kuɗin fansar da ake yi shine ya sanya ‘yan Bindigar ke cigaba da ta’addanci, amma ina da tabbacin muddin aka daina biyan kuɗin fansar komai zai daidaita.

“A ɓangaren gwamnati mu gwammace mu biya diyya ga wadanda iftilain garkuwa da mutane ta faɗa musu akan mu biya kuɗin fansa ga ‘yan bindiga wanda bai da wani amfani”

Mustapha Inuwa ya kuma tabbatar da cewar babu wani tasiri da zaman sulhu da ‘yan bindiga ya haifar illa gagarumar matsala ga gwamnati.

Labarai Makamanta