Daga Waje Ake Ɗaukar Nauyin ‘Yan Bindiga – Audi

Shugaban hukumar NSCDC, Ahmed Audi yace ‘yan bindigan da suka gallabi ‘yan Najeriya suna da masu daukar nauyinsu daga kasashen ketare.


Audi ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin wani taron horarwa na shugabannin jihohi da hukumar tayi a babban birnin tarayya, Abuja.

Taron horarwar wanda kamar yadda hukumar tace, an yi shi ne domin karfafa fannin shugabanci, mu’amala da kuma kwarewa wurin shawo kan tarzoma.


Channels TV ya ruwaito cewa, Audi yace kasar nan na fuskantar babban kalubale, hakan ne yasa ake bukatar hadin kai daga hukumomin tsaro.

“Biyo bayan al’amuran dake faruwa a kasar nan, muna fuskantar tarzomar da a tarihin kasar nan bamu taba gani ba.”Mun taba fuskantar makamantan wadannan tashin hankulan a kasar nan, amma ba sak ba. Wannan al’amarin yana bukatar hukumomin tsaro su hada karfi da karfe wurin kawo karshensa.

“Wadannan mutanen sun dage, wadannan mutanen na da masu daukar nauyinsu daga kasashen ketare. Don haka dole ne mu hada kanmu,” shugaban yace.

Labarai Makamanta