Daga Nahiyar Asiya Sabon Sarkin Zazzau Zai Fito – Shehu Sani

Tsohon Sanata da ya wakilci shiyyar Kaduna ta tsakiya a majalisar Dattawa Sanata Shehu Sani ya tofa albarkacin bakinsa game da wanda ake sa ran cewa zai zama sabon Sarkin Zazzau.

Shahararren ‘dan siyasar ya yi wani magana a kaikaice a shafinsa na Facebook, yayin da ake jiran sanarwar sabon sarki.

Tsohon Sanatan bai kama sunan wanda zai zama sarkin Zazzau ba, amma ya bada satar amsa da ta nuna inda ya dosa.

Kwamared Sani ya rubuta cewa sabon Sarkin da za a nada zai fito ne daga Nahiyar Asiya. Sani ya bayyana wannan ne a shafin sada zumuntansa Facebook a ranar Laraba, 23 ga watan Satumba, 2020.

Daga lokacin da Sani ya yi wannan jawabi da kimanin karfe 6:00 na yamma zuwa yanzu, an yi ta samun martani.

Tsohon ‘dan majalisar bai yi wani karin bayani ba face wannan gajerar magana da ya yi.

Amma masana da sauran masu fashin baki su na ganin cewa Ahmad Nuhu Bamalli ne wanda Shehu Sani ya ke nufi. Dalili kuwa shi ne Ahmad Nuhu Bamalli ya kasance Jakadan Najeriya a kasar Thailand da ke Kudancin Asiya.

Idan za ku tuna sauran manyan masu neman sarautar Zazzau su ne: Iyan Zazzau, Yariman Zazzau, Turakin Zazzau. Daga cikin wadannan ‘ya’yan sarakuna da aka ambata, babu wanda ya ke Asiya ko ma kasar waje sai Magajin Garin Zazzau.

Labarai Makamanta