Da Yiwuwar Ragowar Sauran Fasinjojin Jirgin Abuja Su Mutu – Mamu

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Malam Tukur Mamu wanda ya taimakawa gwamnati wurin sasantawa da ‘yan bindiga suka saki mutane 11 cikin waɗanda su kayi garkuwa a harin jirgin kasa na Abuja-Kaduna yace sauran mutanen dake dajin ka iya mutuwa.

Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda yace macizai na cizonsu kuma ba wata cikakkiyar kulawa suke samu ba, kuma yace nan da ‘yan makwanni zasu iya rasa rayukansu saboda rashin lafiya.

Mamu wanda ya kasance hadimin Sheki Ahmad Gumi ya shawarci gwamnatin tarayya ta tashi tsaye ta gaggauta ceto sauran mutanen dake hannun ‘yan bindiga a dajin.

Amma yace shi ya gama nashi aikin ba zai sake shiga wannan lamarin ba saboda tsaro.

Labarai Makamanta