Da Yiwuwar Gwamnatin Tarayya Ta Ƙara Wa’adin Ɗaukar Ma’aikata 774,000

Gwamnatin tarayya na duba yiwuwar tsawaita wa’adin diban ma’aikata 774,000 zuwa fiye da watanni uku.Karamin ministan kwadago da diban ma’aikata, Festus Keyamo ya bayyana hakan a ranar Litinin, 31 ga watan Agusta, cewa gwamnatin na iya mayar da aikin a matsayin shiri na shekara.

Ya ce wannan sabon hukunci ya biyo bayan korafe-korafen cewa aikin na wa’adin watanni ukun ba lallai ne ya kawo wani sauyi ga wadanda suka amfana ba. Ministan ya kuma nuna karfin gwiwar cewa shirin ayyukan na musamman, wanda zai samar da ayyukan yi ga mutum 774,000 zai cimma nasara.

“Ina da tabbacin cewa shirin zai cimma nasara dari bisa dari. Mun takaita shirin ne zuwa watanni uku ga ma’aikata 774,000 saboda shiri ne mai tsada kuma muna fuskantar faduwa a kudaden shiga,” in ji shi.
“Akwai dabaru da dama da gwamnati ke tattaunawa a kai.

Baya ga haka, gwamnatin na iya tsawaita wa’adin shirin domin mayar dashi na tsawon shekara guda.” idan baku manta ba Festus Keyamo ya bayyana cewa ya riki tsarin raba ayyukan gudan 774,000 kamar yadda gwamnatin tarayya ta bukata.

Keyamo ya bayyana cewa tsarin farko da aka yi na cewa za a ware kaso 15 cikin 100 na ayyukan ga gwamnoni, ‘yan majalisar dokoki, ministoci da kungiyoyi yana nan har yanzu.

Labarai Makamanta