Da Yardar Allah Yaƙin Basasa Ya Ƙare A Najeriya – Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi waiwaye kan yakin basasan da aka kwashe watanni 30 ana yi a Nijeriya kuma ya yi addu’a kada Allah ya maimaitawa Njeriya irin wannan yaki.

Mai magana da yawun shugaban kasan, Malam Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya sake mai taken “Shugaba Buhari ya aika ta’ziyya ga shahidan yakin basasan Nijeriya.”

Nijeriya, karkashin Janar Yakubu Gowon ta shiga yaki da Biyafara da suka balle karkashin jagorancin Laftanar Kanar Odumegwu Ojukwu tsakanin 6 ga Yulin 1967 da 15 ga Junairun 1970.

Shehu ya ce Buhari ya yi waiwayen ne lokacin da ya karbi bakuncin shugaban mazhabar Tijjaniyya, Sheikh Muhammadul Mahy Niass.

Labarai Makamanta