Da Niyyar Aure Nake Kwana Kullum – Adamar Kamaye


Fitacciyar jaruma a Zahra’u Sale, wacce aka fi sani da sunan Adamar Kamaye a cikin shirin Dadin Kowa, ta bayyana matukar bukatar ta ta samun miji domin ta yi aure.

Jarumar ta bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin Dimukaradiyya, dangane da baton auren a gare ta, ?

Sai ta ce ” Ai aure ne ya kawo ni duniya, saboda haka ba zan ki aure ba, domin aure sunnar Manzon Allah ce.”

Ta ci gaba da cewar “Ni kullum da niyyar aure na ke kwana, kuma da ita na ke tashi, don haka ina neman addu’a daga masoya na, da masu yi mini fatan alheri a kan Allah ya kawo mini mijin aure.”

Dangane da mijin da ta ke so ta aure kuwa cewa ta yi;

“ina son miji mai tsoron Allah wanda ya san hakkin aure kuma zai yi kokarin ya sauke shi, don wani lokacin ba aure ba ne ya ke da wahala, samun wanda zai tsaya ya kula da kai tsakani da Allah a nan a ke samun matsala, don haka ina fatan Allah ya kawo mini miji nagari, mai tsoron Allah wanda zai aure ni ya kula da rayuwar auren da za mu yi da shi.” A cewar ta

Labarai Makamanta