Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaba Muhammadu Buhari ya ce Boko Haram wata yaudara da makirci da aka kirkira domin a lalata Najeriya kawai.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin da ya tarbi mambobin kungiyar bishop-bishop na darikar katolika, CBCN, a gidan gwamnati a Abuja.
Shugaba Buhari ya ce za a dora kan cigaban da ya samu a bangaren tsaro, sannan za a mayar da hankali kan tattalin arziki kafin mika mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Buhari ya ce an samu cigaba a bangaren tsaro cikin yan shekarun nan musamman a arewa maso gabas musamman a bangaren gine-gine da ilimi. Ya ce: “Na gode bisa ziyarar da kuka kawo fadar shugaban kasa, na yarda da wasu abubuwan da kuka fada.
Maganar tsaro na da muhimmanci gare mu don idan ba zaman lafiya, ba za a iya tafiyar da kasa ba. “Ban dade da dawowa daga jihohin Adamawa da Yobe ba, Yayin ziyarar jihohin, na saurari abin da mutane da jami’ai suka ce. Duk sun ce an samu cigaba daga 2015 musamman jihar Borno.
“Boko Haram wata yaudara da makirci da aka kirkira domin a lalata Najeriya. Ba za ka iya cewa kada mutane su yi ilimi ba; akwai bukatar mutane su bunkasa ta hanyar ilimi.”
You must log in to post a comment.