Da Gangan Aka Canza Naira Da Karancin Fetur Domin Haifar Da Tarnaki A Zabe – Tinubu

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Dan takarar shugabancin Najeriya ƙarƙashin jam’iyyar APC mai mulki Bola Ahmed Tinubu, ya yi zargin cewar da gangan aka ƙirƙiri batun sauya fasalin wasu takardun kuɗin ƙasar da batun ƙarancin man fetur domin hana gudanar da zaɓen ƙasar da ke tafe.

Bola Tinubu ya yi waɗannan kalamai ne a lokacin gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar da aka gudanar a jihar Ogun ranar Laraba.

“Ba sa son zaɓen ya gudana. Suna buƙatar hana gudanar da shi. Shin za ku bar su?”, in ji Tinubu a lokacin da yake tambayar dubban magoya bayansa da suka halarci taron gangamin a filin wasa na MKO Abiola a birnin Abeokuta.

Tsohon gwamnan na jihar Legas ya yi kira ga ‘yan ƙasar da su yi watsi da batun ƙarancin mai, yana mai shawartarsu da su taka ƙafarsu domin jefa ƙuri’arsu a ranar zaɓen.

Ya ƙara da cewa zaɓen ƙasar da ke tafe zai zama gagarumin sauyi ga ƙasar.

“Sun fara zuwa da batun cewa ”babu mai”. Kada wannan ya dame ku, idan babu man fetur, za mu je da ƙafarmu domin jefa ƙuri’armu”.

“Idan kuna so ku ƙara farashin man fetur, ku ɓoye man, ko ku sauya wa takardun kuɗi kala, amma mu za mu ci zaɓe”, in ji Tinubu.

Labarai Makamanta