Ɗan takarar kujerar Gwamnan jihar Kaduna a ƙarƙashin jam’iyyar APC Honorabul Muhammad Sani Sha’aban yace ko kaɗan bai amince da hukuncin da Kotun daukaka kara dake Kaduna ta ya yi ba na cewar ba ta da hurumin saurarar karar da ya shigar dake ƙalubalantar nasarar Uba Sani inda ta yi watsi da ƙarar, inda ya sha alwashin ɗaukaka ƙara.
Sha’aban ya bayyana hakan ne a yayin zantawa da gidan Jaridar Muryar ‘Yanci ta wayar tarho, inda ya bayyana matakin da zai ɗauka cikin gaggawa kan lamarin.
“Tuni na tattauna da lauyoyi na kan batun inda na basu umarnin sun shirya daukaka ƙara a ranar Litinin kan Kotun ta Kaduna na cewar ba ta da hurumin saurarar karar da aka shigar a gabanta da yin watsi da ƙarar duk da tarin hujjoji da aka gabatar mata”.
Idan jama’a za su iya tunawa a hukuncin da kotun tarayya a garin Kaduna wanda maishari’a Mohammed Garba ya yanke, ya ce tun farko bai kamata akai maganar zaɓen fidda gwani kotu ba.
” Wannan Shari’a ba nan bane huruminta, rashin jituwa ce ta jam’iyya, domin ba akai ga za a ce wai kotu ta saka baki ba. Saboda haka wannan kotu ba za ta saurari wannan kara ba, ta yi watsi da shi.
Hakan ya tabbatar da takarar Uba cewa shine sahihin ɗan takarar gwamna na Jam’iyyar APC a jihar Kaduna.
You must log in to post a comment.