Da Dumi-Dumi: Za A Fara Farautar Almajirai A Kano

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Gwamantin Jihar karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta ce nan ba da jimawa ba za ta fara kama mabarata manya da yara da ke gararamba a jihar.

Gwamantin ta bayyana haka ne ta bakin shugaban hukumar hana barace-barace ta jihar Sheikh Bakari Mika’il, tana mai cewa dukkan yaran da aka kama hukuncinsu zai rataya ne kan iyayensa.

Sannan ta ce akwai tarar kuɗi kamar dai yadda dokar hana bara ta 2013 ta tanada.

Sai dai wasu daga cikin mazauna jihar na bayyana mabambamtan ra’ayi kan tasirin dokar.

Labarai Makamanta