Da Dumi-Dumi: ‘Yan Sanda Sun Ceto ‘Yan Kasuwar Da Aka Sace A Kaduna

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Rundunar ‘yan sandan jihar ta ce ta ceto ‘yan kasuwa 48 da aka sace a kan hanyarsu ta zuwa Kano a hanyar Birnin Gwari Jihar Kaduna ranar Laraba.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige ya fitar a ranar yau Alhamis.

Sanarwar ta bayyana cewa, a lokacin da ayarin motocin ‘yan kasuwar ke tunkarar kauyen Udawa, ‘yan bindiga dauke da bindigogi sun tari ‘yan kasuwar, lamarin da ya kai ga sace da dama.

An ce ’yan sandan da ke rakiya ga ’yan kasuwar sun samu karin goyon baya inda suka yi kaca-kaca da ‘yan bindigan, lamarin da ya kai ga ceto ‘yan kasuwa 48.

“Jami’an tsaro sun yi nasarar ceto mutane arba’in da takwas zuwa cikin aminci. An dauki bayanansu kuma daga baya aka wuce da su inda suka nufa. “Hakazalika, yana da mahimmanci a lura cewa bayanan da ke akwai ga jami’ai sun nuna cewa mace daya ba a same ta ba.

A halin da ake ciki dai ana ci gaba da kokarin ganin an ceto ta lafiya yayin da kuma za a tura karin ma’aikata zuwa yankin domin kare rayuka da dukiyoyin fararen hula a yankin.

Kwamishinan ‘yan sandan ya yabawa jami’an bisa jajircewar da suka yi wajen fuskantar hatsari yayin da suke yi wa kasarsu hidima. Hakazalika, ya nemi su ci gaba da tsayawa tsaf domin fuskantar ‘yan ta’adda da masu aikata munanan ayyuka.

Labarai Makamanta