Rahoton dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Ƴan ta’adda masu fashin daji sun yi garkuwa da ƴan kasuwa sama da guda 70 a kan hanyar su ta zuwa Kano a titin Birnin-Gwari zuwa Kaduna a ranar Laraba.
Jaridar Vanguard ta rawiato cewa an shaidawa manema labarai a Kaduna cewa ƴan ta’addan sun tare jerin-gwanon motocin ƴan kasuwan ne in da daga bisani su ka yi awon-gaba da su cikin jeji.
Jaridar ta ce Rundunar Ƴan Sanda ta jihar ba ta ce komai a kan harin a daidai lokacin da ta wallafa labarin.
Ƙarin bayani na nan tafe…
You must log in to post a comment.