Da Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Yi Gaba Da Daliban Cocin Katolika A Kaduna


Wasu ‘yan bindiga da ake zargi’ masu Garkuwa da Mutane ne, sun kai hari kan Makarantar St. Albert the Great Institute of Philosophy, mallakin Cocin Katolika.

Makarantar karatun tana cikin garin Fayit, dake Masarautar Kagoma na Karamar Hukumar Jama’a ta Jihar Kaduna.

Harin kamar yadda rahotanni suka bayyana, yayi sanadiyar sace daliban da ba a san adadinsu ba.

Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta samu labarin cewa, lamarin ya faru ne a daren Litinin lokacin da ‘yan bindigar suka mamaye harabar makarantar, suna ta harbe -harbe kafin daga bisani su tafi da wadanda abin ya shafa.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalige ya ce, har yanzu bai samu rahoton ba.

ASP Jalige ya bayyana wa Jaridar DAILY POST cewa, “zai tuntubi Jami’in Dan Sandan dake kula da yankin, sannan ya yiwa wakilin Jaridar Karin bayani.

Labarai Makamanta