Da Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Sace Jami’in Kwastam A Zamfara

Rahotannin dake shigo mana daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewa wasu gungun ‘Yan bindiga da ake zargin yaran gogarma Ada Aleru sun yi garkuwa da jami’in Kwastam Mahassan Lawali a karamar hukumar Tsafe jihar Zamfara.

‘Yan bindigan sun arce da Lawali a daren Juma’a a gidansa dake Tsafe.

Wani cikin kannen Lawali, Salim Tsafe ya bayyana wa manema labarai cewa ‘yan bindigan su 50 suka zagaye gidan sannan mutum uku daga cikin su suka shiga gidan suka fito da Alhaji Lawali.

“Maharan sun daure wani abokina da ya zo yin hutun karshen mako a gidan inda suka kwace duk wayoyin sa amma suka sake shi bayan da suka kama Alhaji Lawali.

Wani mazaunin Tsafe Abubakar Bala ya ce ga dukkan alamu ‘yan bindigan Lawali suka zo dauka.

‘Yan bindiga sun bukaci a biya naira miliyan 10.

Bala ya ce ya samu labarin cewa ‘yan bindigan sun kira sun bukaci iyalin Lawali su biya Naira miliyan 10 kafin su sake shi.

Salim ya ce ‘yan bindigan da babban yayansu suke tattaunawa sannan sun cewa duk kudin da suka fada ya kamata a biya ba tare da an nemi ragi ba saboda Lawali mai kudi ne dake da sama da Naira miliyan 100 a hannun sa.

Salim ya ce da aka fada wa ‘yan bindigan cewa Naira miliyan biyar ne za a iya biya sai ‘yan bindigan suka zagi wanda suke maganar da shi sannan suka kashe wayar su.

Ya ce har yanzu ‘yan bindigan basu kara kira ba sannan basu da naira miliyan 10 din da suke bukata.

Salim ya ce sun fara yin adu’o’i domin Allah ya shiga tsakanin Allah ya sa a saki jami’in.

Labarai Makamanta