Sokoto: An Tabbatar Da Mutuwar Fasinja 35 A Motar Da ‘Yan Bindiga Suka Kona

Rahotan dake shigo mana yanzu haka daga jihar Sokoto na bayyana cewa ‘yan bindiga sun kona wata motar fasinja dauke da mutum 42.

Rahotannin sun ce fasinjojin sun fito ne daga karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar domin yin ƙaura zuwa wasu yankunan Najeriya, saboda ta’azzarar ayyukan ‘yan bindiga a inda suke.

Wasu shaidu sun cewa BBC lamarin ya faru ne da misalin karfe 9 na safiyar ranar Litinin.

“Motar ɗauke da fasinjojin ta tashi daga Sabon Birni, ta yi tafiyar da bai fi kilomita shida ba zuwa kauyen Gidan Bawa inda wannan masifa ta afka mata,” kamar yadda wadanda suka yi aikin ceton suka bayyana wa BBC.

BBC ta yi ƙoƙarin jin ta bakin rundunar ƴan sandan jihar, amma haƙarmu ba ta ci cimma ruwa ba, ko da muka kira kakakin, wayarsa a kashe take.

Kazalika an kira kwamishinan tsaro na jihar har sau uku shi ma bai ɗauka ba.

A labarin da muke samu yanzu daga kafar sashin Hausa na BBC na bayyana cewar a zantawar da aka yi da wasu shaidun gani da ido, sun bayyana mutane 35 cikin 42 sun kone kurmus, yayin da mutum 7 suka tsira da munanan raunuka.

Rahoton ya bayyana cewar tuni aka tattara sassan jikkunan matattun kamar kawuna hannaye da kafafuwa inda aka binne su a rami guda.

Labarai Makamanta