Da Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Bindige Dan Majalisar Dokokin Jihar Kaduna

Rahotannin dake shigo mana yanzu daga Jihar Kaduna na bayyana cewar wasu ‘ƴan bindiga sun kashe Alhaji Rilwanu Gadagau wanda shi ne ɗan majalisar jihar mai wakiltar Giwa Ta Yamma.

Wasu makusantansa sun shaida cewa maharan sun yi awon gaba da ɗan majalisar ne tun a ranar Litinin da dare a lokacin da ƴan bindiga suka kai hari a kan hanyar Kaduna zuwa Zaria.

Rahotanni sun ce an ga gawar ɗan majalisar ne a cikin daji a safiyar Laraba.

A ranar Talata ne dai aka samu rahoton cewa ƴan bindigar sun kai hari kan hanyar Kaduna zuwa Zaria inda aka tabbatar da mutuwar mutum ɗaya da sace mutane da dama.

Sai dai mun tuntuɓi rundunar yan sandan jihar Kaduna domin ƙarin bayani ba su ɗaga waya ba.

Labarai Makamanta