Da Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Arce Da DPO

Rahoton dake shigo mana yanzu haka daga Jihar Edo na bayyana cewar wasu tsagerun ‘yan bindiga sun yi awon gaba da babban jami’n ‘yan sanda kuma DPO na ofishin Fugar dake jihar Edo, CSP Ibrahim Aliyu Ishaq.

PRNigeria ta ruwaito cewa ‘yan bindigan sun yi awon gaba da shi ne kusa da Rafin Ise dake tsohuwar hanyar Auchi-Ekperi-Agenebode ranar Juma’a.

Rahoton ya kara da cewa tuni sun tuntubi iyalansa kan maganar kudin fansansa na zunzurutun kudi har naira Miliyan 50.

Labarai Makamanta