Da Dumi-Dumi: Uwar Jam’iyyar APC Ta Dare Gida Biyu

Rahotannin dake shigo mana daga Abuja babban birnin tarayya na bayyana cewar rikicin jam’iyyar APC mai mulki ya bude wani sabon babi ranar Litinin yayin da matasa suka sanar da rushe kwamitin rikon kwarya na Gwamna Buni.

Matasan karkashin kungiyar Progressive Youth Movement (PYM), sun tsaida ranar 26 ga watan Fabrairu a matsayin ranar gangamin taron APC na ƙasa.

Da yake jawabi, sabon shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar APC, Prince Mustapha Audu, wanda ɗa ne ga tsohon gwamnan Kogi, Abubakar Audu, ya bayyana cewa sun fito ne domin ceto APC daga rushewa.

“Yau mun zo rantsar da kwamitin rikon kwarya PYM–CECPC, waɗan nan matasa maza da mata da muka zaba mun ɗora musu alhakin yin duk me yiwuwa wajen ganin mun gudanar da gangami kafin karshen watan Fabrairu, 2022.”

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da, mataimakin shugaba (arewa), Tukur Tukur Buratai, mataimakin shugaba (kudu), Busayo Akinnadeju. Kazalika matasan sun kuma naɗa wakilai daga kowane yankin kasar nan, daga cikinsu har da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, da sauran su.

Da yake martani kan lamarin, mataimakin kakakin APC na ƙasa, Yekini Nabena, yace matasa ba su da karfin ikon rushe kwamitin da Buni ke jagoranta. Ya kuma ƙara da cewa kungiyar matasan ba ta daga cikin mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC (NEC).

Labarai Makamanta