Da Dumi-Dumi: Tinubu Ya Zabi Masari A Matsayin Mataimaki

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu, ya ayyana sunan Alhaji Kabir Ibrahim Masari a matsayin abokin takararsa a zaben shugaban kasa na 2023.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Tinubu ya bayyana sunansa ne a matsayin wanda zai tsaya takara tare dashi yayin da wa’adin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) na jam’iyyu su mika sunayen ‘yan takararsu a zaben 2023 ya kare.

Majiyoyi a sansanin Tinubu da Masari sun tabbatar wa Daily Trust haka ne a yammacin ranar Alhamis. Dan siyasar da aka fitar din ya fito ne daga kauyen Masari da ke karamar hukumar Kafur a jihar Katsina.

Kuma an ce dan uwan Aminu Bello Masari, Gwamnan Katsina na yanzu. Hakazalika, ya taba zama sakataren walwala na jam’iyya mai mulki a zamanin Kwamared Adams Oshiomhole a matsayin shugaban APC na kasa.

Bayan rasuwar ‘Yar’aduwa a 2010, Masari ya koma jam’iyyar maja ta CPC, jam’iyyar da gabanin zaben 2015, ta ruguje tsarinta, inda ta game da wasu jam’iyyu ta zama APC sannan Masari ya koma jam’iyyar mai mulki.

Akwai rahotannin cewa Tinubu zai maye gurbin Masari kafin zabe saboda kawai ya ayyana sunansa ne domin ya cika wa’adin INEC.

Labarai Makamanta

Leave a Reply