Da Dumi-Dumi: Tinubu Ya Tsallaka Faransa

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ɗan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya tafi Faransa domin gudanar da wasu ayyuka, kamar yada wata sanarwa da kakakinsa, Tunde Rahman, ke cewa.

Tunde ya ce ɗan takarar kuma jagoran jam’iyya mai mulki ba zai jima sosai ba a ziyarar da ya kai birnin Paris.

Kafin ya yi balaguron sai da ya gana da shugaba Muhammadu Buhari a fadar gwamnati da ke Abuja.

Sai dai wasu rahotanni da aka fitar a wasu kafofi na cewa Bola Tinubu ya je Faransa ne domin ya duba lafiyarsa.

Labarai Makamanta