Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tsohon dan takarar gwamna a jihar Ekiti, Sanata Gbenga Aluko ya mutu. An ce dan siyasar haifaffen Ode-Ekiti ya mutu ne a ranar Asabar bayan da ya fadi a ofishinsa da ke Abuja.
A cewar Continental Television, an garzaya da shi asibiti inda ya rasu. TVC ta ruwaito cewa daya daga cikin hadiman Aluko da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa gidan rediyon Najeriya cewa Aluko lafiyarsa lau, amma haka dai ya rasu.
Wata majiya ta bayyana cewa marigayin dan siyasar ya rasu ne sakamakon bugun zuciya. Ya kasance da ne ga marigayi masanin tattalin arziki, Farfesa Sam Aluko.
Aluko a shekarar 2018 ya tsaya takarar gwamna a jam’iyyar APC a jihar Ekiti. Aluko wanda aka fi sani da “SGA” ya kasance dan majalisar tarayya tsakanin 1999 zuwa 2003 a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP.
You must log in to post a comment.