Da Dumi-Dumi: Sabuwar Korona Ta Yi Babban Kamu A Fadar Shugaban Kasa

Rahoton dake shigo mana yanzu daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Sabuwar nau’in cutar Korona ta barke a fadar Shugaban kasa, Aso VIlla, inda manyan hadiman Shugaba Buhari da manyan jami’an gwamnati suka kamu da cutar.

An bankado cewa sakamakon gwajin da aka gudanar ya nuna cewa akalla manyan na kusa da Buhari guda hudu sun kamu da cutar. Daga cikinsu akwai Sakataren din-din-din na fadar Shugaban kasa, Tijjani Umar; Dogarin Buhari, ADC Kanal Yusuf Dodo; CSO Aliyu Musa da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu.

Hakazalika akwai Ministan Labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, shima sakamako ya nuna Korona ta hau shi.

Rahoton ya kara da cewa a ranar Laraba, an yakice Garba Shehu da wasu daga taron majalisar zartaswa yayinda sakamakon gwajin PCR ya fito.

Garba Shehu ya tabbatar da cewa lallai ya kamu da cutar Yace: “Ban da tabbacin wadannan mutanen da ka ambata amma na kamu da sabon nauyin cutar maras tsanani. Tun farko ban ji komai ba, la’alla saboda na yi rigakafi sau uku ne, amma yanzu garau nake ji.”

“Amma matsalar cutar nan itace sai abinda masana kimiya suka fada cewa kaji sauki. Yanzu dai ina killace kuma zan koma in sake gwaji don ganin ko har yanzu akwai cutar ko ta tafi.”

Duk yunkurin ji daga bakin Lai Mohammed, Femi Adesina, Tolu Ogunlesi, ya ci tura. Amma majiyoyi masu karfi sun bayyana cewa dukkan jami’an da suka kamu na killace kuma ana kula da su.

Labarai Makamanta