Da Dumi-Dumi: Olukayode Ya Zama Sabon Alkalin Alkalai

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar An rantsar da Mai shari’a Olukayode Arwoola a matsayin muƙaddashin babban jojin kasar, sakamakon murabus da Mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammad ya yi.

Mai shari’a Tankon ya yi murabus ne bisa dalili na rashin lafiya, a wata sanarwa da ya fitar a ranar jiya Lahadi.

Mai shari’a Olukayode Ariwoola shi ne ke bi wa babban jojin Najeriya Mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammad baya – kuma ya sha rantsuwa tare da karɓar ragama a matsayin muƙaddashin babban jojin Najeriya.

Labarai Makamanta