Da Dumi-Dumi: Najeriya Ta Janye Dokar Korona

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ta cire dokar hana fita ta tsakar dare da kuma taruwar jama’a a tarukan bikin aure da na waƙe-waƙe waɗanda aka saka da zimmar yaƙi da annobar korona.

Kwamatin yaƙi da cutar na shugaban ƙasa ya ce an ɗauki matakin ne sakamakon raguwar mutanen da ke kamwua da cutar a ƙasar.

Najeriya ta saka dokokin ne tun bayan ɓullar annobar cikin ƙasar a watan Fabarairun 2020.

Wata sanarwa daga kwamatin ta ce an kuma samu raguwar haɗarin yaɗa sabon nau’in cutar.

Sai dai kuma, ya jaddada cewa wajibi ne mutane su ci gaba da saka takunkumi idan suna cikin wani rufaffen wuri amma bai zama lallai su saka ba idan suna buɗaɗɗen wuri ko kuma fili.

An janye ƙayyadewar adadin mutanen da za su halarci wani taron addini amma kwamatin ya ce lallai ne a saka takunkumi a wurin.

Labarai Makamanta