Da Dumi-Dumi: Mafusata Sun Hana Danjuma Goje Shiga Gombe

Rahotannin da shigo mana yanzu haka daga Jihar Gombe na bayyana cewar wasu da ake zargin yan daba ne, sun hana Sanata Muhammad Ɗanjuma Goje shiga garin Gombe.

Sanata Goje, wanda ya tafi Gombe domin halartar daurin aure, ya dira a filin saukan jirage na Gombe a Lawanti misalin ƙarfe 10.40 na safe.

Wadanda ake zargi yan daban ne sun tare babban titin Gombe zuwa Bauchi kusa da International Conference Centre, sun cinna wuta a titi sun hana shiga ko fita daga Gombe.

Wakilin jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa an fasa gilashin wasu motocci, wasu kuma aka ƙona su, a yayin tarzomar.

Dubban matafiya sun yi cirko-cirko a hanyoyin biyu, duba da cewa babu motar da aka bari ta wuce. An tura jami’an tsaro su kwantar da tarzomar duba da cewa akwai matasa a ɓangarorin biyu ɗauke da makamai.

Bayanai na nuna cewa ba a ga maciji tsakanin Goje da tsohon yaronsa, Gwamna Muhammadu Inuwa musanman a baya-bayan nan kan iko da jam’iyyar APC a jihar.

Labarai Makamanta