Da Dumi-Dumi: Kwamishinar Muhallin Jihar Gombe Ta Ajiye Aiki

Rahotanni dake shigo mana yanzu daga Jihar Gombe na bayyana cewar Kwamishinar muhalli ta Jihar Dr. Hussaina Goje ta ajiye muƙaminta na Kwamishinan muhalli da kula gandun daji.

Rahotanni sun bayyana cewar Kwamishinar ta ajiye aikinta ne saboda wasu dalilai, na raɓin kanta waɗanda ba a bayyana ba.

Sai dai jama’a na danganta ajiye muƙamin nata da hatsaniyar siyasar da aka samu ranar juma’a a Gombe tsakanin magoya bayan gwamnatin jihar da magoya bayan mahaifinta wato Sanata Danjuma Goje.

Indai jama’a ba su manta ba a jiya juma’a tarzoma ta barke tsakanin magoya bayan tsohon Gwamnan Jihar kuma Sanata mai ci Ɗanjuma Goje da matasa masu goyon bayan gwamnatin jihar, lamarin da ya haifar da asarar rayuka.

Labarai Makamanta