Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Umarci Ganduje Ya Biya Sanusi Miliyan 10

Wata babbar kotu a Abuja ta yanke hukunci a biya Sarkin Kano na 14, Muhammad Sanusi II tarar Naira Miliyan 10 saboda aika shi da akayi daga jihar Kano zuwa wata jihar aka killace shi bayan Gwamnati ta sauke shi daga Sarautar Sarkin Kano,

Justice Anwuli Chikere, ne ya yanke hukuncin a yau Talata inda yace dokar masarautar Kano 2019 da akayi amfani da ita wajen killace Sarkin ta ci karo da kundin tsarin mulki na Nigeria 1999.

A cewar Alkali Chikere, kundin tsarin mulkin Nigeria shine gaba da komi don haka hana Sarki Sanusi zuwa Kano ko daukarsa zuwa wani waje haramun ne a dokar Nigeria. Sarkin yana da damar zuwa Kano da duk inda yaso watayawa.

Muhammadu Sanusi ne dai ya shigar da kara gaban Kotu domin kalubalanatar rundunar yan sanda da ta DSS da Gwamnatin Kano killace shi.

Labarai Makamanta