Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Daure Maina Shekaru 61

Wata Babbar Kotun Tarayya a babban birnin tarayya Abuja ta yanke wa tsohon shugaban kwamitin garanbawul a harkar fansho Abdulrasheed Maina hukuncin ɗaurin shekara 61 a gidan yari amma zai yi zaman shekara takwas ne a gidan kason.

Mai shari’a Okon Abang ya yanke wa Maina wannan hukunci ne kan laifuka 12 da suka haɗa da cin hanci da kuma halasta kuɗaɗen haram bayan shigar da ƙararsa da hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon ƙasa EFCC ta yi.

Za a fara lissafa zaman gidan yarin ne daga 25 ga watan Oktoban 2019, wato lokaci na farko da kotun ta aike da Maina gidan kason, bayan da bukatar da lauyoyinsa suka gabatar ta neman beli ta gaza gamsar da kotun.

A wata sanarwa da EFCC ta fitar jim kaɗan bayan yanke wa Maina hukuncin ɗaurin, ta ce wannan lamari wata gagarumar nasara ce a gare ta.

Sanarwar mai sa hannun mai magana da yawun hukumar Wilson Uwujaren ta ce EFCC ta yi nasarar tabbatar da dukkan abubuwan da ake buƙata da suke cikin tuhumar, tare da yanke masa hukunci kan laifuka na 2 da 3 da 6 da 7 da 9 da kuma na 10 na tuhume-tuhumen.

Kazalika kotun ta umarci Maina da kamfaninsa mai suna Common Input Property and Investment Limited da su mayar wa da gwamnatin tarayya da kusan naira biliyan 2.1 da aka gano a asusun ajiyarsu na banki tare da bayar da umarnin rufe kamfanin.

Da farko dai kotu ta samu Maina da ɓoye ainihin wane ne shi tare da sanya jami’an wasu bankuna biyu na Fidelity da UBA da su buɗe masa asusun ajiya ba tare da bin ƙa’ida ba, inda yayin amfani da bayanan wani daga cikin iyalansa ba tare da saninsu ba.

An saka naira miliyan 300 da miliyan 500 da biliyan 1.5 lakadan a cikin biyu daga cikin asusun ajiyar bankunan.

Kotun ta ce Maina ya saci kuɗaɗen ƴan fansho fansho ne waɗanda da “yawansu sun mutu ba tare da cin moriyar wahalar da suka yi ta tara kuɗaɗen ba,” saboda ya gaza bayyana yadda ya samu kuɗaɗen.

Sannan kotun ta ce albashinsa da alawus-alawus ɗinsa a matsayinsa na ma’aikacin gwamnati ba su kai ya tara waɗannan kuɗaɗe da ya mallaka ba.

Kotun ta kuma kama Maina da laifin sayen wata kadara a Abuja wacce ya biya dala miliyan 1.4 lakadan ba tare da biyansu ta banki ba.

A ranar takwas ga watan Oktoba ne kotu ta ɗage sauraron ƙarar bayan da Mai Shari’a Abang ya ƙi amincewa da buƙatar lauyan Maina ta neman a ba da lokaci ya tsara adireshinsa a rubuce, inda lauyan masu shigara da ƙara ya soki buƙatar.

Wata shaida Rouqayyah Ibrahim ta shaida wa kotun yadda Maina ya mallaki kadarori a birnin Dubai na ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa UAE da Amurka da kuma wata kadara da kuɗinta ya kai dala miliyan biyu a unguwar Jabi a Abuja.

Shaidar ta bayyana cewa an ƙwato wasu bayanai har da 32 da ke da alaƙa da kadarorin da Maina da iyalansa suka mallaka a Dubai da Amurka.

Rouqayyah ta kuma ce: “Bincike ya nuna cewa wani kamfaninsa a Dubai Northrich, yana da fiye da motoci 50 da ake masa harkar sufuri da su, sannan yana da wani katafaren gida a wata hamshaƙiyar unguwa a Dubai.

“Matarsa Laila ita ma ta mallaki wani kamfanin tsaftace gidaje mai suna Spotless and Flawless. Sannan mun samu takardun shaidar biyan kuɗaɗe a yayin binciken,” in ji ta.

Shaidar ta kuma bayyana cewa binciken ya tabbatar da cewa wani kamfanin na Maina Kangolo Dynamic, ba ya wata harkar kasuwanci amma sai ya buɗe wani asusun ajiya da sunansa bai fito a ciki ba duk da cewa shi yake da iko da dukkan kuɗaɗen da ake zubawa a ciki.

Ta sake shaida wa kotun cewa wani binciken ya nuna kamfanin Colster Logistics mallakin Maina na da asusun ajiya a bankin Fidelity wanda aka zuba masa fiye da dala 400,000 daga lokacin da aka fara binciken.

Sannan an ƙwato naira miliyan 500 dasga asusun ajiyar kamfanin Kangolo Dynamic cikin shekarun da Maina ke jagorantar kwamitin yi wa fansho garanbawul.

A ranar 10 ga watan Disamban 2020 ne Abdulrasheed Maina ya faɗi a kotu, lamarfin da ya tursasa Mai Shari’a Abang ɗaga ƙarar har sai ranar 21 ga watan Disamban 2020.

Sannan akwai lokacin da ya tsere daga ƙasar bayan ba da belinsa amma jami’an tsaro suka kama shi a jamhuriyar Nijar aka mayar da shi Najeriya don ci gaba da fuskantar shari’a.

Labarai Makamanta