Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Bada Umarnin Garkame Shugaban EFCC A Kurkuku

Babbar Kotun tarayya dake birnin Abuja ta bada umarni wa Shugaban ‘yan Sandan Nigeria IGP Usman Baba Alkali ya gaggauta kama shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) Abdulrashid Bawa.

Alkaliyar da ta jagoranci zaman Kotun Justice Chizoba Oji tace Abdulrashid Bawa yayi biris da umarnin Kotu na ranar 21-11-2018 inda Kotu ta umarni hukumar EFCC ta dawo da wata Mota kirar Range Rover da kuma kudi kimanin Naira Miliyan 40 ma wanda ya shigar da kara amma hukumar ta ki.

Don haka Abdulrashid Bawa da yake shugabantar hukumar a yanzu shi ma ya bijire wa umarni Kotu tare da raina kotu, don haka Alkaliyar ta ce a kama shi sannan a tura shi gidan yarin Kuje dake Abuja.

Nijeriya kenan, watakila maciya amana sun juyo kan wannan dan uwa matashi mai kokarin kwatanta gaskiya zasu kawar da shi don suyi abinda suka saba, amma ni kam ina kyautata masa zato sosai

Har ga Allah wannan abin bai kai Kotu ta zartar da irin wannan hukunci ba, tabbas akwai wata boyayyar manufa, tun da aka kafa EFCC ba’a yi shugabanta da ya wanye lafiya ba.

Allah Ya kyauta.

Daga Datti Assalafiy

Labarai Makamanta