Da Dumi-Dumi: Korona Ta Kama Ministan Abuja

Labarin dake shigo mana yanzu daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan Abuja Muhammad Musa Bello ya kamu da cutar korona.

Mai magana da yawun ministan, Abubakar Sani ne ya tabbatar wa BBC da hakan.

A wani saƙo da ministan ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa bayan ya ji alamun rashin lafiya, ya yanke shawarar yin gwaji wanda bayan gwajin aka tabbatar da ya kamu da cutar.

Ministan ya ce a halin yanzu lafiyarsa ƙalau amma yana jin ƙaiƙayi a maƙogwaronsa da kuma jin zazzaɓi da kuma mura mai majina.

Ministan ya kuma bayyana cewa tuni ya killace kansa inda yake ci gaba da shan magani.

Labarai Makamanta