Da Dumi-Dumi: Kogi Ya Hadiye Dandazon Mayakan ISWAP

Rahotanni daga maiduguri babban birnin jihar Borno na bayyana cewar aƙalla mayaƙan ISWAP 25 ne ruwa ya ci su a cikin kogi yayin da rundunar sojin Najeriya ke fatattakar su a yankin Marte da Tafkin Chadi da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Kafar watsa labarai ta PRNigeria ta bayyana cewa jiragen yaƙin Najeriya ciki har da Super Tucano na sojin saman ƙasar sun kai samame a sansanonin ƙungiyar ISWAP a ranakun Laraba da Alhamis.

Wani mazaunin yankin da aka kai samamen ya shaida cewa jiragen saman sun saki bama-bamai a gidajen ajiye makamai na ƙungiyar ta ISWAP.

Wanda ya shaida lamarin ya bayyana cewa jiragen yaƙin sun tarwatsa gidajen ajiyan kayayyaki a Bukar Mairam da Jubularam da Abbaganaram da Chikul Gudu.

Sai dai mayaƙan da suka tsira daga farmakin da aka kai musu a Bukar Mairam da Jubularam sun gudu inda suka yi ƙoƙarin tsallaka wani kogi da ke yankin tafkin Chadi inda a lokacin ne har 25 daga cikinsu suka nutse a ruwa.

Labarai Makamanta