Da Dumi-Dumi: Izala Ta Bada Umarnin Fara Al-Kunuti

Kungiyar IZALA ta bada umurni ga limaman juma’a dana Kamsu salawat da sauran dukkan masallatan Ahlussunah dake fadin Naijeriya da a fara gabatar da addu’oi na Al-Qanut a dukkan masallatayyan. Shugaban kungiyar Sheikh Abdullahi Bala Lau shi ya bada umurnin ta hanyar rubutacciyar takarda ga manema labarai.

Sheikh Bala Lau yace Wannan umurni ya shafi duk wani masallaci mallakar Kungiyar da sauran masallatan Ahlusunnah dake fadin kasar. Haka zalika dukkan Majalis na ilimi da karantarwa da halqoqi na ilimi da haddan Al Qurani Maigirma da duka nauuka na addua, duka muna bada ummurni a ci gaba da yin addu’oi, haka ma mata a gida suma su bi wannan Ummurnin da yawaita azkar da fatan Allah ya tausayawa wannan Alumma.

in munyi Wannan da kyakkyawar niyya muna zaton Allah zai amsa mana yayi maganin ‘Yan ta’adda da masu daukan nauyin su, kuma za’a samu zaman lafiya a yankunan da matsalar tsaro ta shafa insha Allah.

Shehin Malamin yace wannan mataki zai fara aiki ne nan take ba tare da jiran komi ba.

Allah ya mana jagora, ya kawo mana zaman lafiya mai dorewa. Amin

JIBWIS NIGERIA
08-Jumada Ula-1443*
13-December-2021*

Labarai Makamanta