Da Dumi-Dumi – IPOB Ta Ce A Fita Zaben Anambra

Haramtaciyyar kungiyar ta yi barazanar hana harkoki baki daya a yankin kudu maso gabas din daga ranar 5 ga watan Nuwamba. Yanzu-yanzu: Kungiyar IPOB ta saduda, ta soke dokar zaman gida na dole, ta ce a fita a yi zabe a Anambra

Original Emma Powerful, Kakakin IPOB, a ranar Alhamis, ya ce an dage dokar na zaman gida dole domin bawa mutanen jihar Anambra daman fita su kada kuri’a a zaben gwamna da za a yi a ranar Asabar.

Ya ce: “Mutanen jihar Anambra su fita kwansu da kwarkwata kuma cikin lumana su kada kuri’unsu a ranar 6 ga watan Nuwamban 2021, su zabi shugaban da suke ra’ayi kuma kada su yarda wani mutum ko kungiya ko jami’an tsaro ya musu barazana.”

Labarai Makamanta