Da Dumi-Dumi: Igboho Ya Shiga Hannu A Kokarin Tsallake Kasa

Hukumar Tsaro ta DSS ta cafke mutumin da ke ikirarin jagorantar yunkurin ballewar Yarabawa daga Najeriya, Sunday Igboho.

DSS ta cafke Igboho wanda take nema ruwa a jallo ne a lokacin da yake kokarin tserewa daga Najeriya zuwa kasar Jamus.

Kafar yada labarai ta Sahara Reporters ta rawaito cewa an cafke shi ne a birnin Kwatano na Jamhuriyar Benin, a daidai lokacin da yake kokarin guduwa kasar ta Jamus.

Kafar ta kuma rawaito cewa jami’an tsaron kasar ne suka kama shi, kuma ana sa ran za a dawo da shi Najeriya kowanne lokaci daga yanzu.

Kokarin Aminiya na jin ta bakin Kakakin Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS, Peter Afunanya ya ci tura saboda bai daga kira ko amsa wayar da wakilinmu ya yi masa ba.

Labarai Makamanta