Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Tarayya Ta Bada Hutun Maulidi


Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Talata, 19 ga Watan Oktoba shekarar nan, a matsayin Ranar Hutun don yin bukukuwan Eid-ul-Maulud na wannan shekarar, don tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad (saw).

Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, ne ya yi wannan bayanin a cikin wata sanarwar da ya fitar a madadin Gwamnatin Tarayya, inda ya taya dukkan musulmin da ke cikin gida Nigeria da na kasashen waje, murnar bikin wannan shekarar.

Ya gargadi dukkan ‘yan Nigeria da su sanya ruhin soyayya, hakuri da juriya wadanda su ne halayen Annabi Muhammadu (saw), inda ya kara da cewa, yin hakan zai tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar nan.

Mista Aregbesola ya umarci ‘yan Nigeria, musamman Musulmai, da su guji tashin hankali, rashin bin doka da sauran ayyukan aikata laifuka.

Labarai Makamanta