Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Kano Ta Soke Lasisin Makarantu Masu Zaman Kansu

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta dakatar da dukkan lasisin makarantun kudi da ke fadin jihar, har sai zuwa lokacin da aka tantance su.

Sanusi Sa’id Kiru, kwamishinan ilimi na jihar Kano ne ya tabbatar da hakan lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a birnin Kano yau Litinin.

Wannan al’amarin na zuwa ne bayan ‘yan sanda sun gurfanar da mamallakin makarantar Noble Kids a gaban kotu, Abdulmalik Tanko, wanda ya amsa kashe Hanifa Abubakar, yarinya mai shekaru biyar.

A cewarsa, za a kafa wani kwamiti na musamman wanda zai tantance makarantu kuma za ya fitar da wasu matakai da za a yi amfani da su wurin tantance makarantun kudi a jihar.

Hakazalika, ya ce dukkan makarantun masu zaman kansu da ba su cika sharuddan da za a gindaya musu ba, sun tafi kenan, ma’ana ba za a bude su ba.

Labarai Makamanta