Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Rage Kwanakin Aiki

Gwamnatin jihar Kaduna ta rage ranakun ayyukan Gwamnati a jihar zuwa kwana 4 a wani mataki na garambawul da sanya aikin Gwamnatin zuwa wani mataki na zamani.

A wata sanarwa da kakakin Gwamnam jihar Kaduna, Muyiwa Adekeye ya fitar ya ce daga yanzu ranakun aiki a duka fadin jihar ya koma karfe 8 na safe zuwa 5 na yamma Litinin zuwa Alhamis
amma banda ma’aikatan fannin ilimi da lafiya kowance ma’aikaci zai zauna a gida a ranakun Juma’a domin ya kula da iyalansa da wasu ayyukan noma da ga masu sha’awa.

Muyiwa ya ce shirye-shirye sunyi nisa domin ganin su ma fannin ma’aikatu masu zaman kansu sun bi wannan sabon salo na aiki, hakanan su ma ma’aikatan kiwon lafiya da ilimi zasu shiga wannan tsari nan gaba kadan, Elrufai yace suna kokarin zamanantar da yanayin aiki a jihar Kaduna ta yadda za a rika amfani da fasahar zamani wajen gudanar da manyan ayyuka sannan a karshe ya bayyana cewa sabuwar dokar zata fara aiki a ranar laraba daya ga watan desanbar wannan shekara.

Labarai Makamanta