Da Dumi-Dumi: Gwamnati Ta Sanar Da Ranakun Hutun Kirsimeti

Labarin dake shigo mana yanzu daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ta sanar da ranakun 27 da 28 na watan Disambar 2021 da kuma ranar 3 ga watan Janairun 2022 a matsayin ranakun hutun Kirsimeti hade da na sabuwar shekara.

Wannan na fitowa ne daga sanarwar da ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ya fitar a yau Laraba wadda aka rarraba ta ga manema labarai a Abuja.

A cikin sanarwar da ta iso mana da safiyar yau Laraba Ministan ya bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya taya kiristocin Najeriya da ke ciki da wajen kasa murnar Kirsimeti da zagayowar sabuwar shekarar.

“Dole ne mu yi koyi da rayuwar Yesu Almasihu a cikin ayyukansa da koyarwarsa akan Tawali’u, Hidima, Tausayi, Hakuri, Salama da Adalci, wanda haihuwarsa ke nunawa.

Wannan ita ce hanya mafi kyau ta kwatanta Almasihu da kuma bikin haihuwarsa.” Da yake bayyana kalubalen da kasar ke fuskanta, musamman na rashin tsaro, ya roki kiristoci da sauran ‘yan Najeriya da su yi amfani da wannan lokacin domin yiwa kasa addu’o’in alheri.

Labarai Makamanta