Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Da Dumi-Dumi: Gombe Ya Zama Shugaban Kungiyar ‘Yan Fim

HAƊAƊƊIYAR ƙungiyar masu shirya finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) ta naɗa fitaccen jarumi Umar Mohammed Gombe matsayin shugaban riƙo na reshen ta na Jihar Kano.

Naɗin nasa ya biyo bayan kafa kwamitin shugabanni na wucin gadi na jihar da ƙungiyar ta yi bayan aje aiki da tsohon shugaban ya yi kwanan baya.

A cikin sanarwar da shugaban Hukumar Amintattu (BoT) na MOPPAN, Alhaji Sani Mu’azu, ya bayar a daren yau, ƙungiyar ta bayyana cewa ta yi haka ne domin ta cike gurbin da rashin kwamitin gudanarwa na ƙasa na ƙungiyar ya haifar “a daidai wannan lokaci mai muhimmanci.”

Hukumar Amintattun ta kuma naɗa Hajiya Asma’u Sani a matsayin ɗaya daga cikin shugabannin riƙon “da nufin a ƙara wa kwamitin wakilcin mata”.

Sauran ‘yan kwamitin su ne: Yaseen Auwal, Saima Mohammed, Kamal S. Alƙali da Sulaiman Edita.

Hukumar Amintattun ta ba ‘yan kwamitin shawarar cewa, “Idan har akwai wani daga cikin su da ya ke da burin tsayawa takarar wani muƙami a zaɓen da za a yi, to ya gaggauta aje aiki tun kafin ya bayyana burin sa.”

Ta ƙara da cewa, “BoT ta ɗauki reshen Jihar Kano da muhimmanci kamar dai yadda ta ɗauki sauran rassan MOPPAN na jihohi, wanda bai kamata a bar shi a baya ba saboda duk wani abu da wani reshe ya aikata, to zai shafi sauran.

“BoT ta yi amanna da cewa kwamitin riƙon zai iya gudanar da zaɓuɓɓuka a jihar, domin ya na da ƙwarewa.

“Babban aikin da aka ba kwamitin riƙon na Umar Gombe dai shi ne ya shirya zaɓen shugabanni na jihar ba tare da wani jan lokaci ba.”

A ƙarshe, BoT ta yi kira ga dukkan membobin ƙungiyar da ma dukkan masu ruwa da tsaki a Jihar Kano da su ba sabon kwamitin riƙon ƙwaryar dukkan goyon baya da haɗin kai da ya ke buƙata domin ya sauke nauyin da aka ɗora masa.

Exit mobile version