Da Dumi-Dumi: Gobara Ta Lashe Rayuka A Kasuwar Abuja

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Wata mahaukaciyar gobara da ta tashi a unguwar Kubwa da ke wajen birnin tarayya Abuja, ta yi ajalin mutum aƙalla biyar tare da jikkata wasu da dama.

Yara na cikin waɗanda suka ƙone a gobarar a ranar Asabar. Hukumar agaji ta ƙasa NEMA ta ce an tafi da waɗanda suka kone zuwa asibiti.

Rahotanni sun ce gobarar ta tashi ne sakamakon fashewar wani tankin kananzir.

Wutar ta bazu cikin sauri zuwa kasuwar Kubwa da ke kusa, inda ta lalata shaguna da dama.

Labarai Makamanta