Da Dumi-Dumi: Gobara Ta Lashe Gidan Da Ganduje Zai Koma Bayan Barin Mulki

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano yanzu haka na bayyana cewar wata mahaukaciyar gobara ta kone gidan gwamnan jihar Kano mai barin gado Dr. Abdullahi Umar Ganduje wanda ya lashe miliyoyin naira kafin kammaluwarsa.

An rawaito cewa gidan da gwamnan zai koma bayan sallama da mulkin, yana kan titin Miagun, bayan Kano Club, a unguwar Nasarawa GRA.

Gobarar dai ta tashi ne da yammacin ranar Litinin, kuma ta taimaka wajen asarar dukiya mai tarin yawa.

Majiya mai tushe ta shaida cewa gobarar da ta tashi daga sashin da Dakta Ganduje ke kiwon shanu da sauran dabbobi gaba daya ta lashe bangaren, kuma da yawa daga cikin dabbobin sun mutu a gobarar, tare da konewar wasu kadarori na miliyoyin naira.

Da aka tuntubi Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, Abba Anwar, ya shaida cewa ba ya garin, don haka ba shi da masaniyar menene ya faru.

Da yake zantawa da wakilinmu Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusuf, wanda ya tabbatar da barkewar gobarar, ya ce tuni aka shawo kan gobarar a lokacin da ‘yan kwana-kwana suka isa gidan.

Labarai Makamanta