Da Dumi-Dumi: EFCC Ta Tsare Uwargidan Gwamnan Kano

Rahotanni daga ingantattun majiya sun tabbatar da cewa hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annati, EFCC, ta tsare uwar gidan gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a Abuja.

A cewar majiyoyin, Hafsat Ganduje, wacce babban ɗanta ya shigar da ƙorafi a kanta, an gayyace ta don yi mata tambayoyi amma aka tsare ta ranar Litinin da daddare, watakila don ci gaba da binciken ne da safiyar Talata,

Idan za a iya tunawa babban ɗan gwamnan jihar Kano, Abdul’Azeez Umar Ganduje ne ya yi wa mahaifiyar tasa cune a hukumar EFCC bisa zargin karkatar da wasu maƙudan kuɗaɗe, daga bisani ya kwashi iyalinsa zuwa ƙasar Masar (Egypt).

Mun yi ƙoƙarin ji daga wasu muƙarraban gwamnan da hukumar EFCC amma hakan ya ci tura har izuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Labarai Makamanta

Leave a Reply