Da Dumi-Dumi: Dubban Magoya Bayan APC Sun Sauya Sheka Zuwa PDP A Gombe

Rahoton dake shigo mana daga jihar Gombe na bayyana cewar dubban ‘yan Jam’iyyar APC magoya bayan Gwamna Inuwa sun sauya sheka zuwa PDP lamarin da ya jefa tsananin damuwa a fadar gwamnatin jihar.

Da yake karɓar dubban masu sauya shekar a sakatariyar PDP ta jihar, ɗan takarar Kujerar Gwamna karkashin jam’iyyar PDP a jihar Honorabul Muhammad Jibirin Barde, ya ce jama’ar Jihar sun gaji da halin koma-baya da gwamnatin APC ta jefa su ciki, lamarin da ya sanya jama’a ke tururuwa zuwa PDP domin samun mafita.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka sauya shekar, Madam Felicia Moses ta ce irin tururuwa da jama’a ke yi zuwa Jam’iyyar PDP kyakkyawar alama ce dake nuna mutuwar jam’iyyar APC a jihar ta Gombe.

Manyan ƙusoshin PDP a Jihar sun bayyana gamsuwa da tabbacin da suke da shi a kan samun gagarumar nasara a zaɓen Gwamna da za a yi a shekarar 2023, inda suka bayyana gazawar APC ta dukkanin ɓangarori.

Labarai Makamanta