Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya jaddada ƙudirin Gwamanatin Tarayya na magance ƴan bindiga daɗi, gami da kare ƴan ƙasa akan irin duk wani nau’in ta’addanci a Ƙasar.
Buhari ya bada tabbacin a ranar Juma’a a lokacin da tawagar Gwamnatin Tarayya ta kai ziyarar ta’aziyya ga Gwamna Aminu Tambuwal akan kisan matafiya 23 da ƴan ta’adda suka yi, ta hanyar ƙona su.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mai baiwa Gwamnan Sokoto Shawara na Musamman akan kafafen yaɗa labarai Malam Muhammad Bello a ranar Asabar a Sokoto.
You must log in to post a comment.