Da Dumi-Dumi: Buhari Ya Shilla Zuwa Dubai

Rahotanni daga Abuja babban birnin Tarayyar Najeriya na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya kama hanyar zuwa birnin Dubai na Daular Larabawa domin halartar wani taro na zuba jari da haɗin kan duniya.

Sanarwar da fadar shugaban ta fitar ta ce a ranar Laraba shugaban zai tafi Dubai domin halartar taron da aka kira Expo 2020 Dubai.

Sanarwar ta ce taron wanda baje koli ne, dama ce ga Najeriya shiga jerin ƙasashe 190 don ƙulla kyakkyawar alaƙa da ƙawance domin gina kyakkyawar makoma ga Najeriya.

Sannan taron wata dama ce ga wakilan Najeriya su tallata ƙasar musamman ci gaban tattalin arziki da aka samu a shekaru shida da suka gabata a matsayin wani ginshiki na mayar da ƙasar wurin da ya dace ga ƴan kasuwa na ƙasashen waje su zuba jari

Sanarwar ta ce Buhari zai gana da shugabannin Daular Larabawa da suka haɗa da Yarima mai jiran gado na Abu Dhabi Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan da mataimakin shugaban ƙasa Sheikh Mohammed bin Rashid Al Maktoum. Buhari zai kuma gana da ƴan kasuwa masu zuba jari.

Shugaban zai tafi da rakiyar maƙaraban gwamnatinsa da suka ƙunshi ministan harakokin waje Geoffrey Onyeama da na kuɗi Hajiya Zainab Shamsuna Ahmed da ministan tsaro Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya da ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika da kuma ministan noma da raya karkara Mohammad Abubakar.

Sauran sun haɗa da ministan lafiya Osagie Ehanire da na sadarwa Dr. Isa Ali Pantami da sauransu.

Sanarwar ta ce ana sa ran Buhari zai dawo Abuja a ranar Lahadi.

Labarai Makamanta